25 Maris 2021 - 13:29
Iran: Ba Mu Tsammanin Wata Matsalar Tsaro Da Za A Fuskanta A Lokacin Manyan Zabukan Shekarar BanaIran: Ba Mu Tsammanin Wata Matsalar Tsaro Da Za A Fuskanta A Lokacin Manyan Zabukan Shekarar Bana

Babban kwamandan ‘yan sandan jamhuriyar musulunci na Iran ya yi shara da shiri da tanadin da su ka yi domin ganin an kaddamar da manyan zabuka a cikin wannan sabuwar shekara ta hijira shamshiyya.

ABNA24 : Husain Ashtari ya kuma kara da cewa; Bisa hasashen da su ka yi babu wata matsala mai alaka da tsaro da za a fuskanta a lokacin zabukan.

Har iya yau, kwamandan ‘yan sandan na Iran ya tabo shirin da su ka yi domin tabbatar da tsaro a lokacin bukukuwan shigar sabuwar shekara na Nowruz, wanda kuma har yanzu yana ci gaba.

Nan da watanni biyu masu zuwa ne dai za a gudanar da zaben shugaban kasar karo na 13, da kuma zaben ‘yan majalisar karo 60, sai kuma zabukan kananan hukumomi.

Wasu daga cikin zabukan da za a yi a lokacin sun hada da na Majalisar kwararru masu zabar jagoran juyi da sanya idanu akan ayyukansa.

342/